Kasuwanci
Hukumar Kwastom Ta Musanta Dage Haramcin Shigo Da Motaci Ta Seme

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta karyata labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa cewa gwamnatin tarayya ta dage haramcin shigo da motoci ta kan iyakar Seme.
Mista Hussaini Abdullahi, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kwastam (CPRO) reshen Seme ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Seme, Jihar Legas.
Abdullahi ya bayyana cewa hukumar ba ta yi irin wannan sanarwar ba ko kadan, duk da cewa wasu masu tura dakon kaya ne suka rubuta wa gwamnatin tarayya shawarar biyo bayan shawarar da Prince Ademola Adegoroye, karamin ministan sufuri ya bayar.
Ya ce tsohon ministan ya ziyarci kan iyakar ne domin kaddamar da wasu ayyuka a wani lokaci a cikin watan Fabrairu, kuma masu jigilar kayayyaki suka kai masa korafi kan yadda haramcin ya shafe su.
Ya kara da cewa ministan ya shawarci masu jigilar kaya da al’ummar kan iyaka da su rubuta bukatunsu a rubuce.
Kakakin hukumar ta Kwastam ya ce ziyarar da Daraktan Sufurin Jiragen Sama na Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Musa ya kai a baya-bayan nan, ya tabbatar da cewa ma’aikatar ta karbi takardar kuma ta yi aiki da ita ta hanyar mika wa babbar hukuma.
NAN ta ruwaito cewa iyakar Seme na daga cikin iyakokin kasa guda hudu da gwamnatin tarayya ta sake bude ranar 16 ga watan Disamba, 2020 da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ta yi.
Kafin bude iyakokin kasa hudu, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a ranar 21 ga watan Agusta, 2019, ta ba da umarnin rufe iyakokin Najeriya domin dakile fasakwaurin kayayyaki da makamai.