Labarai
Yunusa Yellow Ya Shaki Iskar ‘Yanci Daga Gidan Yari

Matashin da kotu tayiwa hukunci sakamakon auren wata matashiya ba bisa ka’ida ba ya kammala zaman gidan ka so a wannan rana.
A baya dai Yunusa Yellow ya fara zaman gidan kaso ne a Jihar Bayelsa Kafin Daga Bisani a dawo da shi Jihar Kano, bisa yadda wasu rukunin masu fada aji da lauyoyi suka shige gaba kan batun shari’ar tasa.
Yayin tattaunawa da manema labarai da mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali na Jihar Kano Musbahu Kofar Nasarawa ya tabbatar da sakin matashin.
Kakakin hukumar gyaran halin na Kano ya ce bayan dawowar Yunusa Yellow Kano ya samu kyakyawar shaida wurin gudanar da rayuwarsa a gidan.
Yanzu haka dai al’ummar jihar Kano ta kowane bangare, sai taya matashin murna suke sakamakon shaƙar iskar yanci.