Labarai
NAFDAC Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Wani Gurbataccen Lemo
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NEFDAC ta sanar da ‘yan Najeriya kan wani leman kwalaba na Sprite 50cl marasa kyau da ke yawo a Najeriya.
NAFDAC ta ce an gano wannan samfurin ne biyo bayan korafin da mabukatan hukumar suka samu tare da bincikar su daga bangaren sa ido da tallace-tallace na hukumar.
Hukumar ta ce binciken ya nuna cewa sama da akwatuna biyar na kwalaben Sprite 50cl da aka gano sun gurbace.
“An zana samfurin da abin ya shafa na rashin inganci domin yin gwaji a dakin gwaje-gwaje na hukumar NAFDAC.
“Hukumar ta umurci dukkan daraktocin shiyya da ko’odinetocin jiha da su gudanar da sa ido tare da kawar da kwayar cutar.
“Hakazalika, hukumar za ta gudanar da cikakken duban ayyukan masana’antu masu kyau a halin yanzu, don gano abun da ya haifar da gurbacewar tare da tabbatar da bin izinin tallace-tallace.
“Bugu da kari kuma, an umurci kamfanin, (Nigerian Bottling Company Limited (Abuja plant) da ya tattara kayayyakin da ba su da kyau, sannan su kai rahoto ga NAFDAC domin a sa ido sosai,” inji NAFDAC a shafinta na yanar gizo.
Hukumar NAFDAC ta ce kamfanin da ya kera kayan shine Nigerian Bottling Company Limited (Abuja plant) mai lamba AZ6 22:32.
Ya kara da cewa an kera samfurin a ranar 4 ga watan Afrilun 2023.