Labarai
‘Yan Sanda A Kaduna Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Masu Garkuwa Da Mutane Ne

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama (503) da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da ‘yan fashi da makami, satar shanu, kisan kai, barnata titin jirgin kasa da dai sauransu.
Daga cikin wadanda ake zargin sun hada da wani Ismail Mohammed da ke kauyen Maijere Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar wanda ya yi garkuwa da dan uwansa, Kabiru Mohammed bayan ya karbi Naira 120,000 a matsayin kudin fansa daga iyalansa.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a shedikwatar rundunar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige ya shaidawa manema labarai cewa an kama wadanda ake zargin ne tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2023.
Ya bayyana cewa an kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu, bindigogin revolver guda uku, bindigu na famfo guda biyu, takalmin titin jirgin kasa dubu biyu da dari takwas (2,800), da motoci tara na sata iri daban-daban daga hannun wadanda ake zargin.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da babura guda biyu da magazin na AK47 Live Harsashi, Shanu Dari da Ashirin da Tara da Tumaki Takwas.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a jihar Kaduna a halin yanzu yana nuni ne da yadda rundunar ba ta bar baya da kura ba a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Ya kuma tabbatar wa mazauna garin cewa rundunar ‘yan sandan Kaduna ta kuduri aniyar ganin an hana masu aikata miyagun laifuka damar gudanar da munanan ayyukan su a fadin jihar.