Labarai
Wani Jigon NNPP Ya Bukaci Shugaban Kasa Tinubu Ya Kori Shugaban INEC

Wani babban jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da ya kori Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC).
Ya yi magana ne a cikin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin siyasa mai taken Political Paradigm.
Galadima ya zargi shugaban INEC da yin zagon kasa ga ‘yan Najeriya a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Ya ce abin da Yakubu ya yi ya fi “zunuban” Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN) da ke cikin rikici.
“Dole ne shugaban INEC ya tafi, abin da ya yi bai kai abin da Godwin Emefiele ya yi muni ba. Ya hada baki da wasu mutane domin su murguda muradin yan Najeriya. Ya aikata laifi mafi girma da kowa zai magana,” inji shi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karkashin Yakubu ta sha suka sosai kan gazawarta na saka sakamakon zabe kamar yadda ta yi alkawari, lamarin da hukumar zaben ta dora alhakin tabarbarewar fasaha.
A wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Talata, tawagar da ke sa ido kan zabuka ta Tarayyar Turai ta ce amincewar da jama’a ke da ita ga hukumar ta samu matukar illa.
Amma da yake mayar da martani, Festus Okoye, ya ce matsalar da aka samu wajen ɗora zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu a ƙasar, bai kamata ya kawar da dukan zaɓen da aka gudanar a ƙasar baki ɗaya ba.
“Ba daidai ba ne a yi la’akari da dukkan ayyukan hukumar bisa ga kura-kuran da aka samu a sakamakon zaben shugaban kasa,” in ji shi.
Da yake karin haske a hirarsa da gidan talabijin na Channels, Galadima ya shaidawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour cewa suna bata lokaci suna kalubalantar nasarar shugaba Bola Tinubu.