Connect with us

Ilimi

Harkokin Kasuwanci Sun Samu Tsaiko Yayin Da Wata Zanga-zangar Ta Barke

Harkokin kasuwanci da zirga-zirga sun samu tsaiko na tsawon sa’o’i da dama a ranar Asabar din nan a Omuo-Ekiti.

Tsaikon ya zo ne yayin da wasu mutane suka yi zanga-zanga kan batun mayar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya wuri zuwa Ilawe Ekiti, a Jihar Ekiti.

Idan dai za a iya tunawa, kudirin dokar da ke neman kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya Omuo-Ekiti, ya samu ne ta hannun Sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu, Sanata Biodun Olujimi, kuma majalisun biyu na majalisar ta tara ne suka amince da shi.

Masu zanga-zangar wadanda suka hada da matasa, mata da sarakunan gargajiya daga Omuo Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta Gabas.

Mutanen sun bazama kan tituna a ranar Juma’a da safe don nuna rashin amincewarsu da abun da suka kira rashin adalcin da aka yi musu ta hanyar mayar da FCE da aka yi nufin samarwa zuwa wata al’ummar.

Masu zanga-zangar dauke sa kwalaye da rubuce-rubuce kamar: “A Omuo FCE muna tsaye! Ba gudu! Ba ja da baya”; “Dole a gyara wannan zaluncin Ku dawo mana da FCE”; “Kada ku yi wa Peter fashi don ya biya Paul, FCE na Omuo Ekiti ce”, da sauransu.

Matafiya da za su je Abuja da masu bi ta babbar hanyar garin zuwa Legas da Ado Ekiti da kuma jihar Ondo makwabciyarta, sun sha da kyar saboda hanyoyin sun toshe.

Kokarin da rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar kula da ma’aikata ta kasa da sauran jami’an tsaro da aka tsara na tabbatar da doka da oda a kan masu zanga-zangar don ba da damar zirga-zirgar ababen hawa amma lamarin ya ci tura.

Tun da sanyin safiya ne mai martaba sarkin yankin, Oba Nuhu Omonigbehin ya bayar da umarnin kada duk kasuwanni da shaguna da sauran sana’o’i su bude domin nuna rashin amincewa da rashin adalcin da ake yi wa al’umma.

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, wani jigo a yankin, Cif Segun Akanle, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Ekiti, Mista Abiodun Oyebanji da su kawo agajin Omuo Ekiti ta hanyar mayar da Kwalejin ilimi ta Tarayya garin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet