Connect with us

Labarai

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Binciken Gwamnatin Da Ta Gabata

Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa wani kwamitin bincike da zai binciki duk wani rabon fili da kadarorin gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjonsu a zamanin Gwamna Aminu Tambuwal.

Kwamitin mai mutum 5 ya kasance karkashin jagorancin mai shari’a M.A. Pindiga (mai ritaya) yayin da Barista Nasiru Muhammed Binji zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Cif Jacob E. Ochidi, SAN; Alhaji Usman Abubakar da Barista Lema Sambo Wali.

Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamna Ahmad Aliyu ta bayyana cewa, kwamitin zai kuma tantance asusun bankin gwamnati da adadin da aka samu daga sayarwa da kuma gwanjon kadarorin.

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai yi nazari kan yadda aka raba filaye daban-daban a duk fadin jihar ciki har da gidajen gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjo.

An baiwa kwamitin watanni biyu daga ranar zamansa na farko da ya gabatar da rahotonsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet