Labarai
Gwamnan Kebbi Ya Sauke Hadiminsa Daga Muƙamin S.A

Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi ya sauke mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa, Alhaji Babangida Sarki daga nadin nasa biyo bayan wallafa wani hoto na shigar da bata dace ba a ‘Status’ din sa na WhatsApp.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Ahmed Idris ranar Litinin a Birnin Kebbi.
“Gwamnan, wanda ya fusata da wannan mugunyar ci gaban, ya ce mai taimaka masa ya taka dabi’un da’a da zamantakewar al’ummar Kebbi, wanda galibinsu mabiya addinin Musulunci ne.
“Idris ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da ke bata tarbiyya da mutuncin mutanen jihar ba.”
Kakakin ya ce gwamnan ya gargadi dukkan jami’an gwamnatin jihar da su guji yin irin wannan aika-aikar marar kyau a shafukansu na sada zumunta da sauran wuraren taron jama’a.