Labarai
Daruruwan Mutane Ne Suka Taru Domin Gudanar Da Zanga-Zanga A Nijar

Daruruwan mutanen da ke goyon bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar ne suka hallara a ranar Alhamis din nan domin gudanar da wani gangami.
Mutanen sun taru ne a Yamai babban birnin kasar tare da wasu manyan tutocin kasar Rasha.
Daruruwan mutanen suka ui cin ci rundo don nuna goyan baya ga matakin sojojin kasar ta Nijar. Inji kamfanin dillacin labaran AFP.
Masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne a dandalin ‘yancin kai da ke tsakiyar birnin, biyo bayan kiran da kawancen kungiyoyin fararen hula suka yi a ranar da kasar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekara ta 1960.