Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Raba Kayan Tallafi Na Kudin Da FG Ta Bayar
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ce sun samu Naira biliyan biyu daga cikin tallafin da gwamnatin tarayya ta ce zata bayar daga cikin tallafin Naira biliyan 5.
Yahaya, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata a wajen taron raba kayan abinci a fadar Sarkin Gombe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, tun a makon jiya da gwamnan ya kaddamar da rabon kayayyakin a Yalmatu Deba, kwamitin karkashin jagorancin shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Gombe.
Ya zagaya wasu kananan hukumomi tara domin raba kayayyakin jin kai a gidaje, da kuma mazabu.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa kilogiram biyar, buhunan taki biyu da lita biyu na maganin kashe kwari, katon na macaroni ko spaghetti.
A cewar Yahaya, ba za a yi wani abin al’ajabi ba kamar yadda wadanda suka samu labarin bada Naira biliyan 5 na Gwamnatin Tarayya suka dauka.
Inda ya bayyana cewa ya zuwa yanzu N2b ne kawai ya shiga asusun jihar.
Ya ce, “Mun yi ta zagayawa ana rarrabawa a fadin kananan hukumomin 11. Wannan dai wani mataki ne na hasashen abin da Gwamnatin Tarayya za ta bayar domin a samar da jin dadin rayuwa sakamakon halin da jama’a suka tsinci kai saboda cire tallafin mai da ake haifar da matsalolin da yawancinsu ba a saba ba amma yanzu dole mu magance yanzu.
“Don haka ne nake jaddada cewa mutanen da suka samu wadannan dole ne su je su yi amfani da su da kyau musamman idan kana da gona za ka iya amfani da buhunan taki guda biyu don tabbatar da samun wadata a gonar ka.