Labarai
Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar Da Karbar Wani Kaso Na Tallafin FG

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da karbar Naira biliyan biyu daga cikin kudaden tallafi na Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta amince wa jihohi a ranar Larabar da ta gabata.
Kwamishinan yada labarai, al’adu da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Bala Salisu-Zango, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani game da furucin da gwamnatin tarayya ta saki na Naira biliyan 5 ga jihar.
Ya ce, “An jawo hankalin gwamnatin jihar kan labaran da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa gwamnatin tarayya ta saki Naira biliyan 5 ga jihohi domin rage radadi.
“Ina so in bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta samu Naira biliyan 2 kacal domin siyan hatsi da za a rabawa ‘yan jihar.”
Salisu-Zango ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta yi amfani da Naira biliyan 2 wajen siyo buhunan shinkafa 40,000 domin rabawa masu karamin karfi a daukacin rmazabun da ke a fadin jihar.
Ya ce gwamnati za ta kuma yi amfani da kaso na gaba daga gwamnatin tarayya wajen siyan masara domin rabawa ga magidantan da suka cancanta.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar za ta ladabtar da duk wanda aka samu yansaka a son zuciya a aikin raba kayan agajin. NAN