Connect with us

Featured

Kano: Wasu Muhimman Ayyukan Da Gwamna Abba K. Yusuf Ya Gudanar A Kwana 100 Na mulkinsa

A yayin da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ke cika kwanaki 100 akan mulki, tuni gwamnan ya cimma wasu nasarori da al’umma ke alfahari da hakan.

Kakaki Hausa ta ruwaito cewa cikin wasu manyan Ayyukan da Gwamnan ya gudanar sun haɗar da sasanta duk wasu basussukan fansho ga waɗanda suka yi ritaya daga aikin gwamnatin jihar Kano.

A tsawon kwanakin an ƙwato Asibitin Yara na Hasiya Bayero wanda aka siyar ba bisa ka’ida ba, tare da gyara shi zuwa na zamani.

Dakatar da yankarwa Ma’aikata albashin su, da kuma biyan Albashi a duk ranar 25 ga kowane wata.

Tabbatar da samar da ruwan famfo ga gidaje bayan shekaru 8 na rashin ruwa a jihar, buɗewa tare da gyara manyan makarantu guda 26 da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta kafa kuma gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi watsi da su.

Kula da Kiwon Lafiya da Haihuwa kyauta a Asibitin yara na Hasiya Bayero, da biyan Kudin NECO ga Daliban Makarantun Gwamnatin Kano.

Amincewa da Biyan kudin Rijistration ga Daliban Kano 7000 a Jami’ar Bayero, da rage kashi 50% na kuɗin karatu a manyan makarantun jihar Kano.

Haka kuma an dawo da tsarin bayar da tallafin karatu na kasashen waje da na cikin gida na jihar Kano.

Sai kuma amincewa da sake gyara dukkan Makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati baki daya.

Haka zalika an ci gaba da aikin tituna mai tsawon kilomita 5 a wasu daga cikin ƙananan hukumomi 44.

Da amincewa da fitar da Naira miliyan 72 domin kwasa-kwasai 68 a Kano State Polytechnic da amincewa da kwangilar gina titin Zaria akan naira biliyan 3.6.

Amincewa da gyarawa dalibai gadar tafiya a kafa na BUK, Aminu Kano College of Islamic Studies da Saadatu Rimi University of Education.

Waɗannan sune kaɗan daga cikin ayyukan da Mai Girma Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gudanar a cikin kwanaki 100 da fara mulkin jihar Kano.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet