Labarai
NDLEA Ta Kama Wasu Da Ake Zargi Da Mallakar Muggan Kwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar Yobe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka tanawa manema labarai a ranar Alhamis ta hannun babban jami’ar yada labarai na rundunar, Ramatu SB.
Wadanda ake zargin sun hada da Gapchiya Modu mai shekaru 26 da haihuwa wanda aka gano yana da kullin tabar wiwi guda 80 mai nauyin kilogiram 60.
An cafke shi ne a yayin da ake gudanar da bincike a kan hanyar Kano zuwa Nguru.
An kuma kama wani wanda ake zargi Suleiman Mohammed mai shekaru 37 da laifin mallakar tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.0.
“A ranar 5 ga wata. Satumbar 2023, wata tawagar jami’an rundunar NDLEA a Damaturu, lokacin da suke tsayawa a shingen bincike, sun kama wani mai suna Suleiman Mohammed, mai shekaru 37 mai suna bisa samunsa da busasshen ciyawa guda 5 da ake kyautata zaton na wiwi ne mai nauyin kilogiram 5.0, “in ji sanarwar.
Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bukaci jami’an tsaro da jami’an hukumar da su ci gaba da jajircewa wajen ganin an rage bukatu da wadatar magunguna zuwa mafi kankanta a fadin kasar nan.