Connect with us

Labarai

Tsaro: Sarkin Birnin Gwari Ya Amince Da Sauyawa Wasu Hakimai Gundumomi

A ci gaba da kokarin inganta harkar tsaro a Masarautarsa, Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril, Maigwari Il, ya amince da sauya wasu Hakimai biyu a masarautarsa gundumomin mulki.

Wata sanarwa da sakataren masarautar Mukhtar Salisu Muhammad ya fitar kuma aka rabawa manema labarai ta bayyana cewa hakimai biyu za su yi musanyar mukamai.

Sanarwar ta bayyana cewa an dauke Alhaji Yusuf Yahaya Abubakar (Sarkin kudun Birnin Gwari) daga tsakiyar gundumar zuwa gundumar Kuyello.

Yayin da aka mayar da Alhaji Alhassan Alhassan (Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari) daga gundumar Kuyello zuwa gundumar Birnin Gwari ta tsakiya.

Sanarwar ta ce ya kamata a kammala mikawa da kuma karbar ragamar mulki cikin gaggawa.

A halin yanzu, sabon Hakimin Birnin Gwari ta tsakiya Alhaji Alhassan Alhassan (Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari) ya koma bakin aiki.

Alhassan wanda ya samu rakiyar ‘yan uwa da abokan arziki da sauran masu hannu da shuni zuwa sabuwar fadarsa ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin ci gaban masarautar.

Ya ce zai goyi bayan duk wani mataki da sarkin ya dauka na kawo karshen kalubalen tsaro da masarautar ke fuskanta a halin yanzu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet