Connect with us

Labarai

2023: Miliyoyin ‘Yan Najeriya Ne Ke Fama Da Matsalar Yunwa — UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 17.7 ne ke fama da yunwa, kuma adadin na iya karuwa zuwa miliyan 25.

Jami’ar kula da abinci mai gina jiki ta Asusun Tallafawa kananan Yara (UNICEF), Nkeiruka Enwelum, ta bayyana hakan kwanan nan yayin wata tattaunawa ta kwanaki biyu da kafafen yada labarai suka yi kan bayar da tallafin abinci mai gina jiki a Najeriya.

Hukumar kare hakkin yara (CRIB) tare da Ma’aikatar yada labarai da wayar da kan Jama’a ta Tarayya ta shirya tare da hadin gwiwar UNICEF.

A cewarta, jihar Legas, Borno, Katsina da kuma Kano ne suka fi kowacce yawan mutanen da ke fama da karancin abinci a kasar, duk da cewa ta koka da yadda ake fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki a Najeriya.

Kasar, in ji ta, mai yiyuwa ta cimma burin ci gaba mai dorewa (SDG) kan shayar da jarirai nonon uwa ta shekarar 2030 amma ta ci gaba da kasancewa kan gaba wajen cimma SDG2 kan rashin yunwa.

A halin yanzu, Enwelum ta tabbatar da cewa, kimanin yara miliyan 35 a Najeriya na fama da tamowa, inda kasar ke da adadin yaran da cutar ta fi kamari a Afirka, sannan kuma ta biyu a duniya.

“Kusan yara miliyan 35 na yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da tamowa. Kuma daga cikin wannan, miliyan 12 na kange,” inji ta.

Ta kuma danganta matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar nan da talauci, jahilci, da rashin wadataccen kasafi don samar da abinci mai gina jiki.

Tun da farko a nasa jawabin, kwararre kan harkokin sadarwa na UNICEF, Geoffrey Njoku, ya koka da cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi ba sa kashe isassun kudade don magance karuwar matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar.

Daga nan sai ya kara da cewa adadin karancin abinci mai gina jiki a Najeriya ya yi yawa; don haka akwai bukatar a toshe gibin kudade ta hanyar tattara albarkatun cikin gida da kuma kara wayar da kan jama’a daga kafafen yada labarai.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet