Labarai
Gwamnatin Kano Za Ta Haɗa Kai Da Ƙasar Ghana Don Fara Kula Da Haihuwa Kyauta

- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fara ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu a dukkan asibitocin da ke fadin jihar kyauta.
Gwamnan ya bayyana cewa ya fara aikin hada kai da wata kasa a Afirka domin sake karfafawa da inganta ayyukan bayar da lafiya a jihar.
Mun gamu da matsala a fannin gaba daya, inda asibitoci da dama ke gudana ba tare da muhimman magunguna ba.
A kokarin karfafa harkar kiwon lafiya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fara ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu a dukkan asibitocin da ke fadin jihar.
Yusuf ya bayyana cewa ya fara aikin hada kai da kasar Ghana domin sake karfafawa da inganta ayyukan bayar da lafiya a jihar.
Yayin da yake karbar mataimakin ministan lafiya daga kasar Ghana, Alhaji Mahama Seini, wanda ya kai ziyarar aiki Kano a ranar Litinin, gwamnan ya ce ya gamu da matsala a fannin gaba daya, inda asibitoci da dama ke gudana ba tare da muhimman magunguna ba.
“A lokacin da muka shigo, abu na farko da muka fara yi shi ne, mun fara aikin gyaran manyan asibitocin Jiha, yayin da muka sake gina su gaba daya domin samar da yanayi mai kyau na samar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar,” inji shi.
Yusuf ya yi nuni da cewa, domin a magance matsalolin da suke fama da su, musamman a fannin kiwon lafiyar mata masu juna biyu, gwamnati ta fara gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu kyauta a dukkan asibitocin da ke fadin jihar.
Gida-Gida ya kara da cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin sake gyara daukacin wuraren kula da lafiya a matakin farko dake kananan hukumomi 44 na jihar baki daya.
Da yake tsokaci kan alakar Najeriya na tsawon shekaru da Ghana, Mataimakin Ministan Lafiya na Ghana, Seini ya ce, “Najeriya da Ghana suna da kyawawan kamanceceniya na gargajiya, wanda ke nuna karara ‘yan uwantaka, da ke wanzuwa tsawon shekaru.”
Yusuf ya bayyana shirinsa na yin hadin gwiwa da Ghana a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, ababen more rayuwa da ilimi.
Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba tun bayan hawan gwamnatinsa kwanaki 100 da suka gabata.
“Tun lokacin da ake zato, muna aiki tukuru don tabbatar da ingantacciyar isar da sabis a fannin kiwon lafiya.
“Tun daga lokacin gwamnatinmu ta samar da kiwon lafiyar mata masu juna biyu kyauta, da kuma gyara asibitocin jihar, nan ba da dadewa ba za ta fara gyara dukkanin manyan asibitocin jihar,” in ji Gwamnan.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara gudanar da ayyukan dakunan shan magani na tafi da gidanka, yana mai jaddada cewa an riga an sayi motoci da kayan aikin asibitocin.
Seini ya ce sun je Kano ne domin karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu.
Ya ba da tabbacin cewa Ghana ta himmatu wajen ganin an cimma manufofin da aka sanya a gaba.