Labarai
Wani Matashi Ya Samu Gurbi A Gidan Gyaran Hali Bisa Umarnin Kotu

Wani matashi mai shekaru 22 mai suna Halifa Sani ya gurfana a gaban wata kotun shari’ar musulunci ta jihar Kano bisa zarginsa da aikata munanan barna.
Wanda ake tuhumar na zaune a Gadon Kaya Quarters, da ke Kano, yana fuskantar tuhuma guda daya da laifin haddasa mummunar barna.
Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Ismail Nuhu, ya kai karar lamarin a ranar 12 ga watan Satumba a ofishin ‘yan sanda na Mandawari da ke Kano.
Ya yi zargin cewa a ranar da misalin karfe 8:00 na dare, wanda ake kara ya samu sabani da wanda ya kai karar wanda ya kai ga cin mutunci.
Wada ya ce wanda ake tuhumar ya fusata, ya dauki wuka ya daba wa mai karar a hannunsa, wanda ya raunata shi.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 120 da 158 na kundin laifuffuka.
Sai dai wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya bayar da umarnin tsare shi a wani gidan gyaran hali.
Lawal-Abubakar ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari’ar. NAN