Labarai
Majalisar Dokokin Yobe Ta Amince Da Kudurin Kafa Hukumar Hisba

Majalisar dokokin jihar Yobe ta amince da kudirin kafa hukumar da ke umarnin da kyaķkyawa da hani da mummuna ta Hisba a jihar.
An zartar da dokar ne a ranar Laraba domin tabbatar da hukumar da ke umarni da Kyakkyawa da hani da mummuna.
A cewar shugaban kwamitin, Yakubu Suleiman, kafa hukumar Hisba zai taimaka wa gwamnati wajen ganin an aiwatar da tsarin shari’a yadda ya kamata domin tsarkake al’umma daga duk wata munanan dabi’u da laifuka.
Suleiman ya yabawa ’yan majalisar bisa gudunmawar daban-daban da suka bayar wajen samun nasarar kudirin dokar Hisba.
DAILY POST a baya ta rahoto cewa Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta amince da rahotan zaunannen kwamitinta mai kula da harkokin shari’a, shari’a da kuma harkokin addini a kan kudirin dokar kafa hukumar Hisba a jihar.
Majalisar ta amince da rahoton ne bayan tattaunawa mai zurfi kan shawarwari 41 na kwamitin.