Connect with us

Labarai

FRSC Ta Gargadi Magoya Bayan Jam’iyyu Yayin Da Ake Dakon Sakamakon Zaben Kano

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen jihar Kano ta gargadi magoya bayan jam’iyyar APC da NNPP da su guji “murnar amutu ko ai rai” a lokacin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yanke hukuncin a ranar Larabar nan.

Kwamandan sashin, Ibrahim Sallau-Abdullahi ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai ta hannun kakaki hukumar FRSC Labaran Abdullahi a Kano.

“Magoya baya su bijirewa murnar amutu ko ai rai a lokacin da aka yanke hukunci a kotun kararrakin zabe, musamman ma da ababen hawa ko kawo cikas a kan tituna.

“Murnar amutu ko ai rai na iya haifar da saba ka’idojin zirga-zirga da kuma haifar da cikas ga manyan tituna da kuma hadarurruka a kan tituna, saboda masu aikata laifin za su fuskanci fushin doka,” inji shi.

Rundunar ta ce jami’anta da sauran jami’an tsaro ba za su lamunci tukin ganganci, rashin mutunta dokar hanya, tukin kwaya da barasa a wuraren ajiye motoci ba, ba tare da tsangwama ba, da wuce gona da iri, da kuma tukin mota a lokacin da kuma bayan hukuncin kotun.

Ya shawarci masu ababen hawa da su bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa.

NAN ta rawaito cewa a yau ne kotun zata yanke hukunci. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet