Labarai
Kotu Ta Ayyana Gawuna A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Hukumar zabe mai zaman Kkanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Abba K. Yusuf wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Yayin da Nasir Gawuna, abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC ya taya shi murna, sai dai jam’iyyarsa ta garzaya zuwa kotu.
A ranar Larabar nan ne kwamitin alkalai mai mutum uku ya bayar da umarnin janye takardar shaidar cin zabe da INEC ta mika wa Gwamna Abba tare da bayar da takardar shaidar cin zabe ga Gawuna.
Kotun ta cire kuri’u 165,663 daga jimillae kuri’un Gwamna Yusuf da ya samu, inda ta bayyana cewa takardun kuri’un zaben (165,663) ba su da tambari ko sanya hannu, don haka ta bayyana cewa ba su da inganci.