Labarai
DSS Ta Kama Matashiyar Da Ta Yi Barazanar Kai Harin Kunar Bakin Wake

Rundunar tsaro ta farin kaya ta cafke wata matashiya mai suna Fildausi Ahamadu mai shekaru 23 da haihuwa, bisa zargin yin barazanar kai harin kunar bakin wake kan alkalan kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano, wadda ta soke zaben Gwamna Abba Yusuf a kwanakin baya.
Wata majiya mai karfi a hukumar ta DSS ta shaida wa jaridar Punch a ranar Talata cewa Firdausi Ahamadu an dauke ta ne biyo bayan wani faifan bidiyo da aka dauka a ciki tana barazanar kai harin kunar bakin wake.
KARANTA LABARIN ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Kansila A Katsina, Yan Sanda Sun Tabbatar
A cikin faifan bidiyon, an ji matar, sanye da jar hula kuma tana magana da harshen Hausa, tana kuma barazana ga dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna, wanda ya yi nasara a kotun, inda take maganar kai hadarin saka masa bam.
“Kada ku kuskura ku nuna wurin da ku ke, in ba haka ba, ban damu ba sai na saka rigar bam don na kashe kaina da ku,” in ji ta.
Ta kuma ambaci sunan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, inda ta dora laifin sakamakon kotun a kansa.
Majiyar DSS ta ce, “Hakika muna tuhumar Fildausi Musa Ahamadu a kotu domin bai kamata a dauki wannan barazanar da wasa ba”.
Pingback: Kano: Hukumar Kula Da Asibitoci Ta Rufe Wani Asibitin Bisa Rashin Bin Ka'idojin Aiki - KAKAKI HAUSA