Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da ‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Kansila A Katsina

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Talata ta ce ta fara gudanar da bincike kan kisan wani kansila da aka yi a karamar hukumar Funtua.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe marigayin mai suna Samaila Mairago a daren ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Nasarawa Quarters a Funtua.

Mazauna yankin sun ce shi kansila ne mai wakiltar gundumar Nasarawa ta karamar hukumar.

KARANTA LABARIN Kotu Ta Kori Gwamnan Sule Ta Ayyana Dan Takarar PDP A Nasarawa 

An bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki garin ne a daren ranar Litinin inda suka nufi gidansa.

Rahotanni sun ce an harbe marigayi kansilan ne a gidansa.

Ba a iya tantance ko ‘yan bindigar sun tafi da dukiyoyinsa bayan harin ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin.

Sai dai ya ce har zuwa safiyar ranar Talata ba a kama su ba.

“Mun fara bincike kan lamarin. Ya zuwa yanzu ba a kama su ba amma za mu ci gaba da bayyana halin da ake ciki, yayin da bincike yake ci gaba da gudana,” inji Aliyu.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: DSS Ta Kama Matashiyar Da Ta Yi Barazanar Kai Harin Kunar Bakin Wake - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet