Connect with us

Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Ziyarci Jami’ar Jihar, Inda Ya Bada Tabbacin Ceto Daliban Da Aka Sace

 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro na bakin kokarinsu wajen ganin an ceto daliban jami’ar tarayya ta Gusau da aka sace.

Ya kuma yi alkawarin samar da isasshen tsaro a jami’ar domin samar da tsaro ga daliban don su ci gaba da gudanar da harkokinsu na ilimi ba tare da fargabar kai hari ba.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis din nan yayin da yake gudanar da aikin tantance al’amuran tsaro a jami’ar da muhallinta, biyo bayan sace dalibai mata sama da 30 da aka yi a unguwar Sabon Gida.

Lawal, wanda ba ya nan a lokacin da lamarin ya faru, kuma bayan dawowarsa jihar nan take ya ziyarci jami’ar ta tarayya da ke Gusau domin duba halin da ake ciki tare da karbar bayanai daga mahukuntan makarantar ta yadda za su hada kai wajen karfafa tsaron jami’ar.

Tashar Talabijin ta Channels ta rawaito cewa Ya dauki lokaci yana jawabi ga daliban, inda ya bukace su da kada su bari wannan yanayi mara dadi ya dakusar da jajircewarsu wajen ci gaban karatunsu.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Shugaba Tinubu Mutum Ne Mai Kyakkyawar Manufa Ga Najeriya - Shattima - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet