Siyasa
Shugaba Tinubu Mutum Ne Mai Kyakkyawar Manufa Ga Najeriya — Shattima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Alhamis ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da zaman lafiya da bunkasa yankin Arewa maso Gabas, inda ya ce Bola Tinubu yana da kyakkyawar manufa da alheri ga Nijeriya.
Shettima ya karbi bakuncin shugabannin hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) karkashin jagorancin shugabanta, Manjo Janar Paul Tarfa, wadanda suka zo gabatar masa da shirin tabbatar da zaman lafiya da cigaban yankin arewa maso gabas (NESDMP) a fadar shugaban kasa ta Villa, da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Shettima ya ce, “Shugaban na da nufin alheri ga kasa. Ana sanyawa Bola Tinubu ran alkhairi; Ba zan daina faɗin haka ba.”
KARANTA LABARIN Gwamnan Zamfara Ya Ziyarci Jami’ar Da Aka Sace Dalibanta
Shugabannin Arewa maso Gabas sun gabatar da daftarin dabarun ci gaban Arewa maso Gabas ga mataimakin shugaban kasar.
Shettima wanda ya lura da cewa tawagar ta kunshi manya-manya na shiyyar arewa maso gabas, ya ce a lokacin shekarun su, suna fafutukar ne domin ‘ya’yansu da jikokinsu kawai ba don wata bukata ta kudi ba.
Ya kuma tabbatar wa kungiyar cewa takardar dabarun ci gaban arewa maso gabas za ta kai ga manajan daraktan hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) cikin sa’o’i 48 za ta je ga Tinubu.
Da yake tunawa da ziyarar da hukumar ta NEDC suka kai masa a ranar Larabar da ta gabata da suka gabatar masa da wani babban shiri na ci gaban yankin na tsawon shekaru 10, Shettima ya jaddada bukatar samar da shugabanci na gaskiya.