Connect with us

Tsaro

Sojojin Sama Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Tare Da Lalata Maboyarsu A Borno Da Zamfara

 

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce farmakin jiragen sama na Operation Hadin Kai da Hadarin Daji sun kawar da ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da suke kai a matsugunan su da ke yankin.

NAF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ranar Lahadin nan a Abuja.

Gabkwet ya ce da sanyin safiyar ranar Asabar ne rundunar ta kai harin sama a wata maboyar ‘yan ta’adda da aka gano a Bukar Meram, kusa da yankin tafkin Chadi a jihar Borno.

Ya ce hare-haren ya zama dole bayan an tabbatar da cewa ‘yan ta’addan da suka yi gudun hijira daga Suwa zuwa yankin Bukar Meram a baya-bayan nan, domin su samu sake kai hare-hare kan sojojin kasa da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

A cewarsa, an ba da izinin kai hare-hare ta sama a yankin Bukar Meram domin murkushe ‘yan ta’addan.

“Sakamakon martanin da aka samu bayan harin ya nuna cewa an cimma sakamakon da ake sa rai saboda an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da aka lalata babura sama da 40 da manyan bindigogi shida,” in ji shi.

Kakakin rundunar NAF ya ce an kai hare-hare irin wannan ta sama kan ‘yan ta’addan a ranar 11 ga watan Oktoba da rundunar sojin sama na Operation Haradin Daji ta kai wa yankin Sangeko da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Ya ce ‘yan ta’addan wadanda ke cikin ayarin babura kusan 70 a kan titin Kabaro zuwa Sangeko, sun yi arangama da su tare da kashe su, inda ya ce an lalata musu babura tare da jikkata wasu ‘yan bindigar.

Gabkwet ya ce babban hafsan hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya yaba da kwarewa da kwazon yadda aka gudanar da aikin.

Ya ambato Abubakar yana cewa, “Kokarin da kuke ba sojojin kasa abin yabawa ne. Ku mai da hankali kuma kada ku yi sakaci domin dole ne mu ci gaba da baiwa ‘yan kasarmu kwarin gwiwar don su cancanci ci gaba.” NAN

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantgrandpashabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwingrandpashabet güncel girişjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetgrandpashabetsahabetsahabetgrandpashabet güncel girişcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetgrandpashabet girişpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet