Connect with us

Labarai

Zamfara: Sojoji Sun Kubutar Da Daliban Jami’ar Gusau Da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Rudunar sojojin saman kasar nan karkashin Dakarun Operation Hadarin Daji tare da hadin gwiwar jami’an ‘yan sandan jihar Zamfara sun ceto daliban jami’ar tarayya da ke Gusau (FUGUS) guda hudu da aka yi garkuwa da su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya fitar a Gusau ranar Lahadin nan.

Dakarun Operation Hadarin Daji tare da ‘yan sandan jihar ne suka ceto daliban jami’ar tarayya Gusau (FUGUS) guda hudu da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su a dakunan kwanan dalibai da ke unguwar Sabongida ranar Asabar.

An samu nasarar ceton daliban ne bayan da sojojin suka amsa kiran da aka yi musu a kan lamarin.

Ba tare da bata lokaci ba kuma sojojin suka tattara tare da kafa wani shingen bincike akan hanyar wanda yasa akayi dauki ba dadi tsakanin sojojin Najeriya da yan bindigar.

“Daga nan ne muka fi karfinsu sai ‘yan ta’addan suka yi watsi da wadanda lamarin ya rutsa da su da misalin karfe 12 na dare, inda daga bisani sojoji suka kubutar da su” Yahaya ya bayyana.

A baya-bayan nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da dalibai 25 ‘yan makaranta daya da ma’aikatan 9 da ke unguwar.

Jami’an tsaro sun ceto dalibai 13 da ma’aikata 3 yayin da sauran wadanda harin ya rutsa da su ke a hannun ‘yan bindigar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet