Featured
Neja: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mai Unguwa, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama

Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban kauyen Zagzaga da ke unguwar Kabula a karamar hukumar Munya a jihar Neja, Malam Usman Hussaini.
Jaridad PUNCH ta samu labari daga majiya mai tushe cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan mai unguwa kauyen, inda suka fitar da shi suka harbe shi har lahira.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata bayan da musulmi suka yi sallar isha a ranar. ‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutanen kauyen da dama, galibinsu mata da kananan yara.
A turmutsutsun da ya biyo bayan mamayar da ‘yan fashin suka kai sama da 50, da dama daga cikin mutanen yankin sun samu raunuka, kuma a yanzu haka suna karbar magani ko dai a babban asibitin garin Sarkinpawa, da ke shedikwatar karamar hukumar ko kuma a gidajen ‘yan gargajiya.
A cewar majiyoyin al’umma, yanzu haka duk garin babu kowa inda ‘yan bindigar suka mamaye yankin.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, Salihu Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, “Mun samu rahotanni irin haka, muna jiran mutuminmu da ke yankin ya yi mana cikakken bayani.
Ya kara da cewa, “Bayan samun rahoto daga wurin, za a aika da rahoto ga gwamnatin jihar.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba domin tabbatar da faruwar lamarin.