Connect with us

Featured

Yara Biyu Sun Mutu, Wasu Kuma Sun Jikkata Sanadiyyar Gobarar Da Ta Tashi Cikin Kwale-kwale A Neja

Wani hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar yara biyu tare da jikkata wasu mutane biyu a karamar hukumar Katcha da ke jihar Neja.

An ce jirgin ruwan ya kama da wuta ne biyo bayan wata matsala da injinsa ya samu wanda ya kona wata harkar man fetur da aka ajiye a cikin jirgin.

Babban Darakta na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Salihu Garba ne ya bayyana haka a wani sakon WhatsApp da ya aike wa jaridar Punch a ranar Asabar din nan, inda ya ce lamarin ya faru ne da karfe 6 na yammacin ranar Juma’a.

A cewar Garba, jirgin na dauke da fasinjoji 145.

“NSEMA ta samu rahoton wani hatsarin jirgin ruwa wanda ya yi sanadin mutuwar yara 2 tare da raunata mutane 2 a karamar hukumar Katcha.

“Lamarin ya faru ne a jiya 20/10/2023 da misalin karfe 6 na yamma inda injin kwale-kwalen ya kama da wuta sakamakon rashin aikin na’urar tare da kona wata jarkar man fetur da aka ajiye a cikin jirgin wanda ke dauke da mutane 145.

“Mutanen ’yan kabilar Danbo ne a Jihar Kogi, suna kan hanyarsu ta dawowa daga Kasuwar Katcha.

“Ya zuwa yanzu, an gano gawa daya yayin da ake ci gaba da neman ta biyun,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet