Featured
Aliko Ɗangote Zai Raba Kayan Abinci Ga Mabukata Albarkar Watan Ramadan

Fitaccen mai arzikin nan kuma ɗan kasuwa Alhaji Aliko Dangote zai tallafawa mabuƙata da kayan abinci don saukaka musu daga halin matsin tattalin arzikin da ake ciki don yin azumin watan Ramadan cikin nishadi.
Ƴarsa Hajiya Fatima Aliko Ɗangote ce ta bayyana hakan, yayin wani taron ganawa da yan Jaridu na Arewacin Najeriya daya gudana a birnin Kano.
Hajiya Fatima ta ce mahaifinta ya jima yana gudanar da ayyuka domin kyautata rayuwar alummar jahar Kano, shi yasa a wannan lokaci ya kudiri aniyar tallafawa mabukata da kayan abinci sakamakon halin kunci da matsin rayuwar da ake ciki
Ga wadanda Ke bibiyar ayyukan jinkai na Gidauniyar Dangote suna sane da yadda ake gudanar da ayyukan inganta rayuwar Jama’a a asibitoci da Makarantu baya ga bayar da abinci ga mabukata tsawon shekaru.