Featured
An Karrama Wasu Jami’an Sojojin Najeriya, Bayan Kin Karbar Cin Hanci

Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) da ke aiki da rundunar soji ta musamman wadda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, sun ki amincewa su karbi cin hancin Naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a Filato.
Jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin James Oya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa menema labarau a ranar Larabar nan a Jos.
Oya ya ce, sojojin da ke aiki a sashi na hudu, sun kuma kama wasu da ake zargin barayin ne da suka ba su cin hanci.
Ya bayyana cewa jami’an takwas da suka ki karbar cin hancin ba iya yabo za a yi musu ba har da karramawa.
Kamfanin dillacin labarai na Kasa ya rawaito cewa, Kwamandan rundunar Manjo-Janar Abdusalam Abubakar wanda ya yaba wa sojojin bisa jarumtaka da kuma abin koyin da suka yi, ya bukaci sauran jami’an tsaro da su yi koyi da wannan gagarumin yunkuri na kare rayuka da dukiyoyi a jihar.