Featured
Buhari Ya Yabawa Tinubu A saƙon Murnar Ƙarin Shekara

Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar ƙarin shekara, inda ya roƙa masa lafiya da tsahon kwana, ta yadda yan Najeriya za su cigaba da amfana da kyakkyawan jagorancin sa.
A saƙon taya shugaba Tinubu murnar cika shekara 72 da Shugaba Buhari yayi ta hannun mai Yaɗa labaran sa Malam Garba Shehu, Buhari ya jinjinawa Tinubu wajen magance matsaloli da yawa a fadin kasar.
“Ni da iyalina muna maka fatan alheri da adduar tsahon kwana domin samun ayyukan cigaba a kasa”.