Featured
Sarkin Musulmi Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka Da Sallah

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya taya ɗaukacin al’umma barka da Sallah yayin da musulman Najeriya suka gudanar da sallar idi ranar Laraba.
Sultan kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin shari’ar musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ja hankalin al’ummar musulmi su ci gaba da neman ilimi domin kyautata imaninsu.
Sarkin ya kuma buƙaci musulmi su sanya shugabanninsu a addu’o’in su domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.