Featured
Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Jam’iyyar ADC

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rufe ɗaya daga cikin ofisoshin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da ke jihar, bisa hujjar kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnatin ta ce matakin ya biyo bayan wani rikici da ya haɗa da wasu magoya bayan jam’iyyar da mutanen da ta kira bata-gari.
Read Also : Mahanga TV appoints former AREWA24 staff Zuwairiyah Girei as MD
Kwamishinan Filaye da Gidaje na jihar, Lauya Nasiru Dantsoho, ya sanar da rufe ginin a ranar Litinin. Ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne bayan nazarin takardun mallakar ginin.
Dantsoho ya ce binciken ya nuna cewa ginin mallakin tsohuwar bankin Savannah ne, kuma babu wani sauyin mallaka da aka yi wa rajista a hukumance. Ya ce matakin na da alaƙa da rikicin da aka samu kwanan nan tsakanin wasu magoya bayan jam’iyyar da bata-gari.
Pingback: Na yi addu'a ga dukkan ƴan Najeriya a lokacin da nake Ibadar Umara - Tinubu - KAKAKI 24