Connect with us

Featured

EFCC Ta Kwato Miliyoyin Naira A Binciken Da Take Yi Wa Sadiya Umar Farouq Da Beta Edu

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa ta’annati EFCC ta ce tana bincikar wasu shugabannin bankuna da aka gano hannunsu a badaƙalar kudaden ma’aikatar jinƙai da ta sa aka dakatar da Beta Edu daga matsayinta na minista.

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce, a halin yanzu, “ana gudanar da bincike kan bankunan da ke alaka da badaƙalar.

“Manajojin daraktocin bankunan sun ba da muhimman bayanai game da badakalar,” wadda kawo yanzu ita ce mafi daukar hankali a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Oyewale ya kara da cewa hukumar EFCC ta kwato karin kimanin Naira miliyan 534 kimanin Dala 445,000 abinciken da take wa dakatacciyar ministar agaji, Beta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar Farouq.

Hukumar ta bayyana cewa har yanzu babu wanda ta wanke cikin Sadiya ko Beta Edu da sauran jami’an ma’aikatar daga zargin almundhanar da suke fuskanta.

Kakakin na EFCC, Dele Oyewale, ya ce Dala 445,000 da kuma Naira biliyan 32.7 da hukumar ta kwato daga matan biyu wani ɓangare ne na kudaden tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba wa ma’aikatarsu domin rage raɗaɗin talauci a tsakanin ’yan Najeriya.

A cewarsa, kuɗaɗen sun hada na tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, da aka dawo wa Najeriya da su daga ƙasashen waje.

Sauran sun haɗa da kuɗaɗen tallafin COVID-19 da kuma rancen da Najeriya ta karɓo daga Bankin Duniya da aka ba wa ma’aikatar domin raba wa al’ummar ƙasa tallafin rage raɗaɗin talauci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet