Connect with us

Featured

Wani Rikicin Sojoji Da Masu Adaidaita Sahu Ya Yi Sanadiyyar Rasuwar Mutum Uku Da Jikkatar Wasu

Mutane uku ake fargabar sun rasu wasu 10 sun samu raunukan harbi a rikicin sojoji da direbobin baburan A Daidaita Sahu a garin Gashua, da ke Karama Hukumar Bade ta Jihar Yobe.

A ranar Lahadi ne aka ba hammata iska bayan wata motar sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke aikin sintiri ta yi taho-mu-gama da wasu masu baburan Adaidaita Sahun, inda wani direban baburin da fasinjojinsa suka samu raunuka.

Hatsarin da ya auku a Gadar Gashua da ke kusa da garin ya fusata jama’ar yankin inda suke zargin sojojin da gudun wuce kima da tukin ganganci da kuma rashin bin dokar hanya.

Wani shaida ya bayyana cewa a sakamakon haka ne matasa wadanda akasarinsu masu baburan ne suka fara zanga-zanga, suka tare babban titin zuwa Gashua.

“A sakamakon haka ne sojoji suka mayar da martani ta hanyar yin harbi, har aka samu rasuwar mutum daya a wurin,” in ji shi.

Wani ganau kuma dan jarida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce hukumomin Asibitin Kwararru da ke Gashua sun tabbatar da rasuwar mutane uku daga cikin wadanda aka harba.

Dan jaridan ya kara da cewa wasu mutum 10 sun samu raunuka daga harbin da sojojin suka yi, yawanci a kafafunsu.

Mataimakin kakakin Rundunar Operation Hadin Kai da ke Damaturu, Kyaftin Shehu Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce suna jiran rahoton jami’insu da ke kula da yankin da abin ya faru.

Sanata Ahmad Lawan, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, ya bukaci hukumomin soji su binciki lamarin domin daukar matakin da ya dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet