Featured
An Dakatar Da Gudanar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Jihar Gombe — Kwamishina

Gwamnatin jihar Gombe a ranar Juma’ar nan ta sanar da cewa ba za a gudanar da aikin tsaftar muhalli da aka tsara a kowace ranar Asabar di karshen wata ba a gobe saboda zaben kananan hukumomi.
Da yake bayyana hakan a Gombe, babban birnin jihar, Kwamishinan Ruwa, Muhalli da Albarkatun Daji, Mohammed Fawu, ya yi kira ga mazauna yankin da su kiyaye tsaftar muhallin su, yana mai jaddada cewa kada su jira lokacin da aka ba su gaba daya domin shiga harkar tsaftar muhalli.
Ya ce, “Wannan don sanar da jama’a ne cewa an dakatar da aikin tsabtace muhalli na wata-wata, wanda aka saba a kowace Asabar ta karshen watan a iya watan Afrilu 2024.
“Wannan shi ne domin gudanar da zaben kananan hukumomin da aka tsara a ranar 27 ga watan Afrilun 2024 a jihar Gombe. Ana kyautata zaton dakatar da aikin tsaftar muhalli na wannan wata zai share fagen gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a gobe Asabar.”
Muhammad Fawu ya ce an dakatar da mazauna yankin ne domin ba su damar zabar jami’an karamar hukumarsu, inda ya kara da cewa, “Don haka ana shawartar jama’a da su yi amfani da wannan dakatarwar su fito domin kada kuri’a a ranar Asabar 27 ga Afrilu za a gudanar da zaben kananan hukumomin.”
Shima da yake nasa jawabin, babban sakataren hukumar kare muhalli ta jihar Gombe, Auwal Baba-Jada, ya bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin ware karin wuraren tattara shara guda 90.
“Muna da karin 90 da za mu gina ba kawai a Tumfure ba amma tare da Liji, Akko hanyar wucewa da za ta zama wuraren tattarawa,” in ji Baba-Jada.