Featured
Mutane Uku Sun Rasu, Biyu Sun Jikkata A Ginin Da Ya Rufta A Kano — NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu biyu a wani ginin bene mai hawa uku da ya rufta a unguwar Kuntau Quarters da ke karamar hukumar Gwale a Kano.
Dokta Nuradeen Abdullahi, ko’dinetan hukumar NEMA na Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma adadin wadanda suka mutu a ranar Juma’ar nan a Kano.
“Mun sami kiran waya mai cike da tashin hankali yau da misalin karfe 9:20 na safe daga wani mutumin kirki cewa wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya ruguje a unguwar Kuntau.
“Da samun bayanan, mun aika da tawagarmu da gaggawa wurin da abin ya faru.
“Ya zuwa yanzu, an ceto mutane biyar, kuma an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka tabbatar da mutuwar uku daga cikinsu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka, kuma suna samun kulawa.” Inji Abdullahi.
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a cikin ginin.
“Tawagar NEMA da hukumar kashe gobara ta jihar Kano da ‘yan sanda da Red Cross da NSCDC da SEMA da dai sauran su na a wurin da lamarin ya faru domin tabbatar da an ceto sauran mutanen da suka makale,” in ji Abdullahi (NAN).