Connect with us

Featured

Cutar Ƙyanda Ta Laƙume Rayukan Mutane 42 A Jihar Adamawa

Akalla mutane 42 ne suka rasa ransu sakamakon kamuwa da cutar ƙyanda a ƙananan hukumomin Mubi da Gombi a Jihar Adamawa.

Kwamishinan lafiya da ayyukan jin ƙai, Feliɗ Tangwame ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Juma’a.

Felid Tangwame ya bayyana cewa, cutar ƙyanda ta ɓarke a unguwanni 8 na Mubi da kuma unguwanni 7 na Gombi, inda ya ƙara da cewa “ adadin waɗanda suka mutu ya kai 42 daga cikin 131 da kuma 177 da suka kamu da cutar a Mubi da Gombi.”

Duk ƙananan hukumomin jihar in banda Lamurde an sanya su a matsayin waɗanda cutar za ta iya ɓulla.

Sai dai Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta ɗauki matakin shawo kan cutar, domin ta ma shawo kan lamarin cikin gaggawa.

Ya ce, gwamnati da abokan hulɗarta na sanya ido sosai a kan lamarin, don haka ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da ɗaukar matakan da suka dace akan cutar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet