Connect with us

Featured

Wani Harbin Bindiga Ya Samu Dan Jarida A Gidan Gwamnatin Kano

 

Wani dan jarida wakilin gidan Talabijin na Abubakar Rimi, ARTV a gidan gwamnatin jihar Kano, Naziru Idris Ya’u, harsashi ya same shi a gidan gwamnatin jihar a wani harbi da akai zargin daga nesa aka yo shi.

Majiyarmu ta tattaro cewa tushen harsashin da har yanzu ba a san shi ba ya samu wakilin ARTV a cikin gidan gwamnati da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, a ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara.

Nazir Ya’u wanda a nan take aka garzaya da shi asibitin gidan gwamnati, an ce har yanzu ba a san asalin daga inda harsashin da ya same shi yake ba.

An sallami dan jaridar da ya samu rauni daga baya bayan an yi masa magani.

Wani ma’aikacin lafiya a asibitin ya ce dan jaridar ya yi sa’a saboda harsashin da aka harba ba daga kusa aka harbo shi ba.

Bayan afkuwar lamarin, jami’an ‘yan sanda da ke gidan gwamnati sun fara gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga fadar gwamnatin Kano dangane da harbin.

Sai dai shirun da aka yi kan lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce da rashin kwanciyar hankali a tsakanin ‘yan jarida, lamarin da ke nuna irin hadarin da ‘yan jarida ke fuskanta hatta a wuraren da ake zaton na da tsaro.

SolaceBase ta tuntubi Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Asabar amma layin wayarsa bai shiga ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet