Featured
Gwamnatin Kano Ta Musanta Harbin Harsashi Ga Dan Jarida A Gidan

Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton harba wani harsashi da aka ce ya samu mai raahoto a gidan gwamnati a yammacin ranar Juma’a.
Jaridar Alkiblah ta ruwaito cewa, wani dan jaridar gidan talabijin na Abubakar Rimi, Naziru Idris Ya’u da ke rahoto a gidan gwamnatin Kano, ya samu harbin bindiga a yammacin ranar Juma’a, a gidan gwamnatin.
Ba a dai san daga inda harsashin ya samo asali ba saboda an garzaya da dan jaridar da ya jikkata zuwa asibitin gidan gwamnati.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Daraktan yada Labaran Gwamna, ya fitar a ranar Asabar, ya musanta faruwar lamarin inda ya bayyana shi a matsayin mara tushe.
Sanarwar ta kara da cewa, “An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan wani rahoto da ya fito daga kafafen yada labarai na yanar gizo da ke nuna cewa wani dan jarida gidan Talabijin na jihar da ke gidan gwamnati ya samu wani harbin harsashi.
Lamarin da ya faru an samu bambanccin bayanan, wanda ya haifar da fargaba da cece-kuce game da lafiyar ‘yan jarida da ke yada labarai a gidan gwamnati.
‘’Don a fayyace, Naziru Yau, wakilin gidan talabijin na jihar, babu wani harsashi da ya same shi.
‘’Maimakon haka, ya samu raunuka daga tarkacen karfen da ya fitowa daga wani gini da ake ci gaba da yi a gidan gwamnatin jihar Kano, yankin da aka killace domin aiki.
Sai dai binciken SolaceBase ya nuna cewa lamarin ya afku ne a masallacin da ke kusa da kofar shiga gidan gwamnati a rukunin da aka kebe domin yin alwala, kamar yadda wanda abin ya shafa ya tabbatar.
A kan haka, babu wani gini da ake yi a kusa da wajen sai dai aikin da ake yi yana nan a bayan ofishin gwamnan da ke kusa da African House a gidan gwamnati.
Hakazalika, a wata tattaunawa ta WhatsApp da manema labaran gidan gwamnati suka yi a ranar Asabar, kan yadda labaran ya kasance a gaban ganau, hoton yana nan.
An sanar da SolaceBase tabbatacce cewa an kuma kai wakilin asibiti a safiyar yau don ci gaba da kula da shi.
Sai dai ana ci gaba da bincike kan tushen harsashin.