Connect with us

Featured

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 25 A Wasu Kauyukan Jihar Katsina

Wasu. ‘Yan bindiga sun kashe mutane 25 a wani farmaki da suka kai wasu ƙauyuka 4 a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar nan, martani da suka yi ga hare-haren da sojojin ƙasar suka kai maɓuyarsu, kamar yadda majiyoyi a yankin suka bayyana.

Ƴan bindigar sun kutsa kauyukan Unguwar Sarki, Gangara, Tadi da Kore a gundumar Sabuwa ta jihar Katsina a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, a cewar kwamishinan tsaron jihar, Nasiru Babangida.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke ɗanɗana kuɗarsu a hannun ‘yan bindiga da ke cin karensu babu babbaƙa a arewa maso yammacin ƙasar, inda suke kisa tare da satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Mazauna ƙauyukan da dama ne suka samu rauni sakamakon waɗannan hare-hare, a yayin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da mutane da dama daga cikin su.

RFI ta rawaito cewa Rahotanni sun ce akasarin waɗanda suka mutu ƴan sa-kai ne da ke bai wa al’ummominsu kariya daga ayyukan ƴan bindiga masu kisa da satar mutane.

Yawancin al’ummomi a arewa maso yammacin Najeriya sun kafa ƙungiyoyin sa-kai don yaki da ƴan bindiga da suka hana su sakat, sakamakon rashin wadatuwar jami’an tsaro.

Masana harkar tsaro dai sun yi ittifakin cewa waɗannan ƴan bindiga ba su da wata aƙida, kuma su na samun ƙwarin gwiwa ne kawai daga kuɗin da suke samu a satar mutane, saia dai sun bayyana damuwa a kan yadda ake ci gaba da samun haɗaka tsakanin ƴan bindiga da ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet