Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Rage Wa Masu Amfani Da Band A Kudin Wutar Lantarki

Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta rage kudin wutar ga masu amfani da layin Band A.
NERC ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki da su rage kudin kowane kilowatt daga Naira 225 zuwa Naira 206 ga kwastomomin da ke kan layin Band A.
Umarnin na daga cikin matakan da hukumar ta dauka da nufin tabbatar da samun wutar lantarki ta akalla awa 20 a kullum ga ’yan Band A.
Sanarwar da Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas ya fitar ya ce ragin zai fara aiki ne daga ranar 6 ga watan nan na Mayu, 2024, amma bai shafi kwastomomin da ke kan layin lantarki na Band B, C, D da kuma E ba.
Ragin N19 da aka yi wa ’yan Band A na zuwa ne kimanin wata guda da ta yi musu karin kudin kilowatt daga N68 zuwa N225, wanda ya sha Allah-wadai daga al’umma da wasu mahukunta.