Featured
NDLEA Ta Kama Wasu Dilolin Miyagun Kwayoyi A Najeriya

Hukumar hana sha da Fataucin miyagun ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wasu manya-manyan dilolin ƙwayoyi da wiwi a jihohin Najeriya.
NDLEA, ta gano wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta ƙasa da ƙasa a sassan Najeriya da ke da alaƙa da Afirka ta Kudu da kuma ƙasar Thailand.
Aƙalla mambobin ƙungiyar biyar ne aka kama a wani samame na tsawon makonni biyu da hukumar ta gudanar a jihohin Legas, Abia da Anambra, bayan ƙwace haramtattun kwayoyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
Jami’an NDLEA da ke bincike a kan hanyar Abuja zuwa Abaji a ranar Laraba 1 ga watan Mayu, sun kama wata tankar iskar gas makare da buhunan tabar wiwi 511 mai nauyin kilogiram 4,752.
An ɗakko buhunan wiwi ɗin ne daga jihar Ondo za a kawo Abuja domin ci gaba da rarrabata ga mabuƙata.
Hukumar ta kuma kama wasu matsa masu shekaru 22 da kuma 25 dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 207.1 a Zaria, jihar Kaduna ranar Litinin 29 ga watan Afrilu.
Sai wani matashi dan shekara 35 da aka kama da kwalabe 194 na maganin tari a unguwar Hotoro a Jihar Kano.
A jihar Bauchi, jami’an NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Bauchi zuwa Jos sun kama wa wani dan shekaru 39 dauke da kwalaben codeine 595, da kwayoyin tramadol, rohypnol da diazepam da yawansu ya kai guda 38,260.
jihar Benue a ranar Afrilu da an kama wani da kunshin wiwi guda 66 da nauyinta ya ka kilo 33.
Shugaban NDLEA Birgediya Buba Marwa ya jinjina wa dakarun hukumar tasa bisa wannan namijin ƙoƙari wurin zaƙulo da tabbatar da an kamo duk wani mai sha ko safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.