Featured
Dan Wasa Mbappe Ya Sanar Da Kawo Karshen Kwantiraginsa Da PSG

Tauraron ‘dan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya sanar da cewar a karshen wannan kakar zai kawo karshen zaman sa na shekaru 7 a kungiyar PSG, ba tare da bayyana kungiyar da zai koma ba.
Mbappe yace wannan shekarar itace ta karshe a wurin sa a kungiyar PSG, saboda ba zai sabunta kwantiragin sa ba, kuma zai buga wasan sa na karshe a ranar lahadi mai zuwa a karawar da za su yi da kungiyar Toulouse.
Kungiyar masu hada magunguna ta yi zanga-zangar adawa da cin zarafin da NDLEA ke yi a Kaduna
Fitaccen ‘dan wasan ya koma PSG ne daga kungiyar Monaco a shekarar 2017, inda ya yi fice wajen lashe gasar kwallon kafar Faransa har sau 6, bayan wanda ya lashe tare da kungiyar Monaco.
Mbappe ya kuma lashe kofin kalubalen Faransa har sau 3 a shekarar 2018 da 2020 da kuma 2021.
Filato: Ƴanbindiga Sun Hallaka Makiyaya 2 Da Shanu 150
Yayin bugawa PSG wasanni ne Mbappe ya yi fice tare da zama tauraro wajen lashe kofin duniya da kungiyar kwallon kafar Faransa a shekarar 2018.
Sai dai wannan kakar mai karewa ta zo masa da kalubale da dama sakamakon kin rattaba hannu na tsawaita kwangilarsa wadda ta kare bara, abinda ya kai ga aje shi a wasannin PSG.
Duk da yake ‘dan wasan bai bayyana inda zai sauya sheka ba, amma rahotanni da dama daga kafofin yada labaran Faransa sun ce tuni ya kulla yarjejeniya da kungiyar Real Madrid domin komawa daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.