Featured
Najeriya za ta tura Sojoji kasar Gambia domin aikin wanzar da zaman lafiya

Rndunar sojan Najeriya a yau Juma’a ta sanar da tura sojoji 197 domin shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Gambia.
Babban jami’in ayyukan sojan Najeriya, Manjo Janar Boniface Sinjen ne ya bada sanarwar a Jaji dake jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin 197 sun fara daukar horo a ranar 4 ga watan Mayu a cibiyar Martin Luther Agwai dake Jaji a jihar Kaduna.
An baiwa jami’an sojin horo kan dabarun wanzar da zaman lafiya.