Connect with us

Featured

KEDCO ya yanke wutar Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil kan bashin Naira Miliyan 248

Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote dake garin Wudil na cikin matsanancin yanayi biyo bayan yanke wutar makarantar da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO yayi.

Kamfanin KEDCO ya yanke wutar jami’ar ne makwo guda da ya wuce bisa bashin kudin wuta da ya kai Naira Miliyan 248.

Da yake yiwa manema labarai bayani kan halin da makarantar take ciki, shugaban sashin kula da lamauran dalibai na jami’ar, Farfesa Abdulkadir Dambazau ya ce duk wani yunkuri na jawo kan hankalin kamfanin KEDCO na mayar da wutar makarantar yaci tura inda kamfanin ya dage sai an biya bashin kudin wutar.

Acewar, Dambazau daga yunkurin da suka yi har da biyan Naira Miliyan 20 wanda ya ce shi ne kudin wata da gwamnati ke baiwa jami’ar.

Jami’ar wacce take da yawan mutane 28, 000 a cewarsa na fama da matsaloli masu tarin yawa ciki har da na samar da ruwan sha.

Ya ce wutar lantarki na da matukar muhimmanci ga jami’ar kasancewarta ta kimiyya da fasaha.

Farfesan ya kuma ce lamarin zai kara tsananta ne idan dalibai suka dawo daga hutun da suke.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet