Featured
Gwamnatin Kano za ta gina dakunan karatu a kananan hukumomi 44
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na samar dakuna karatu masu dauke da kayayyaki na zamani a kananan hukumomi 44 dake jihar.
Shugaban hukumar kula da dakunan karatu na riko na jihar, Malam Sulaiman Hodi Adamu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Adamu ya ce aikin samar da dakunan karatun za a yi shi ne domin sake farfado da dabi’ar yin karatu da bincike tsakanin dalibai.
Ya ce hukumar ta gudanar da ziyarar duba dakunan karatu na gwamnati a kananan hukumomi 23 cikin 44 na jihar.
Ya ce ziyarar wani bangare ne na sake farfado da dakunan karatun domin su dawo aiki.
Shugaban hukumar na riko ya ce a bayan kammala ziyarar, za su mika rahoto ga ma’aikatar ilimi domin kafa dakunan karatun a kananan hukumomi 44.
Sannan ya jaddada kokarin gwamnatin jihar mai ci wajen bunkasa harkar ilimi don gyaran goben matasa.
“Gwamnatin jihar Kano ta bai wa hukumar mu goyan baya na rangadi ga dakunan karatu da ake dasu a kananan hukumomi 23.
” Mun je domin duba yanayinsu da sake farfado da su.
“Wannan shirin zai sake fito da dabi’ar yin karatu tsakanin dalibai”.
