Featured
Kotu ta umarci tsohuwar ministar Buhari ta yi bayanin yadda ta kashe Biliyan 729 ga Talakawa Miliyan 24

Babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas ta umarci tsohuwar ministan jinkai da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq tayi bayani dalla-dalla kan yadda aka rabawa Talakawan Najeriya Miliyan 24.3 kudi Naira biliyan 729 a tsawon watanni 6.
Kotun ta kuma umarci tsohuwar ministan ta bayar da jerin sunaye da bayanan wadanda suka amfana da tallafin ciki har da jihohin da suka fito.
Mai shari’a, Justice Deinde Isaac Dipeolu ne ta yanke hukuncin biyo bayan karar da aka shigar na neman bayani wacce kungiyar SERAP ta gabatar.
Kungiyar ta samu kwafin shari’ar na ainihi a ranar Juma’a.
A hukuncin da ta yanke mai shari’a Dipeolu ya ce ” Dokar bayar da bayanai ta tilastawa tsohuwar ministan bada bayani ga kowanne mutum ciki har da SERAP. a don haka nake bada umarnin gaggawa ga tsohuwar minista ta bada bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe Naira Biliyan 729 ga Talakawan Najeriya Miliyan 24.3 a shekarar 2021″.
Mai shari’ar ta kuma umarci tsohuwar ministan “ta bada bayanai ga SERAP kan yadda aka zabi wadanda suka amfana da shirin da kuma hanyar da aka bi wajen biyan kudin”.
Sannan ta umarci Sadiya Umar-Farouq tayi bayani kan tsarin biyan Naira dubu 5 ga talakawa Miliyan 24.3 wanda ya kasance kaso 5 na kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021″.