Featured
Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Jarida 2 Da Iyalansu A Kaduna

‘Yan bindiga sun sace shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai na jihar Kaduna, AbdulGafar Alabelewe da iyalansa guda 3.
Lamarin ya faru ne a daren jiya a Danhono dake Millennium City a jihar Kaduna.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun sace wakilin jaridar Blueprint, Abdulraheem Aodo da matarsa a dai unguwa.
AbdulGafar Alabelewe shi ne wakilin jaridar The Nation a jihar ta Kaduna.