Featured
An kama ma’aurata dake shirin siyar da dansu domin tafiya kasar waje

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da kama wasu ma’aurata bisa zargin yunkurin siyar da dan su mai shekaru 2 domin tafiya kasar Canada.
Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau Alhamis.
Hundeyin ya ce ma’auratan an kama su ne a ranar Talata yayin da suke kokarin siyar da yaron nasu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce a ranar Talata da misalin karfe 2:45 baturen ‘yan sanda na Isolo ya samu bayani kan cewa wasu ma’aurata sun je babban asibitin Isolo inda suka bayyana aniyarsu ta siyar da dansu.
“Bayan samun rahotan, jami’an ‘yan sanda sun gaggauta zuwa asibitin inda suka tarar suna daf da siyar da yaron”.
” Ma’auratan da aka sakaya sunansu sun amsa laifunsu inda ake ci gaba da bincike”.